Adamawa: An Shawarci Manoma Da Neman Ingantaccen Iri

An kirayi Manoma da su kasance masu neman ingantaccen iri domin shukawa a gonarsu domin ganin an samu cigaba da bunkasa harkokin noma a fadin Najeriya baki daya.

Babbar Kodinetan sashin noma na Agriculture Biotechnology a Najeriya kuma uwar gidan Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Jihar Adamawa Mrs Rose Maxwell Gidado ce tayi wannan kira a lokacinda take jawabi a wurin taron karawa juna sani na kwana biyu da aka shiryawa manoma a Yola.

Dr Rose Maxwell tace samun inganceccen iri yana da matukan muhimmanci ga manoma don haka ya kamata Manoma su maida hankali wajen neman samun inganceccen iri wanda a cewarta hakan zai taimaka wajen cigaba da bunkasa harkokin noma yadda ya kamata.

Tace an shirya taron karawa juna sani ga manoman ne domin wayar musu da kai dangane da yadda zasu fahinci yadda ake gudanar da harkokin noma a zamanance wanda a cewarta yanzu noma ya zama sana’a don haka ya zama wajibi manoma su maida hankali wajen rungumar harkokin noma yadda ya kamata.

Dr Rose ta kuma yaba da yadda gwamnatin jihar Adamawa ta maida hankali wajen harkokin noma wanda a cewarta hakan zai taimaka musammanma wajen rage rashin aikin yi a tsakanin Matasa.

Shima anashi jawabni Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda mataimakinsa Crowther Ceth ya wakilta ya yaba da irin wannan taron bita da aka shiryawa Manoman, wanda yace yanzu noma shine kan gaba don haka dolene a baiwa sashin noma muhimmanci.

Da yake zantawa da muryan yanci Alhaji Manu Ngurore wanda kuma manomi ne yace yaji dadi matuka da shirya wannan taron domin a cewarsa haka zai karawa manoman kwarin gwiwa wajen gudanar da harkokin noma a fadin jihar dama kasa baki daya.

Labarai Makamanta