Adamawa: An Shawarci Kiristoci Da Koyi Da Halayyar Yesu Almasihu

An kirayi mabiya addinin kirista a jihar Adamawa da suyi koyi da halayen Yesu Almasihu domin samar da hadin kai dama wanzar da zaman lafiya a tsakanin Al’umma baki daya.

Shugaban kungiyar kiristoci a Najeriya shiyyar jihar Adamawa, Bishop Stephen Dami Manza ne yayi wannan kira a lokacin da yake magana da manema labarai dangane da yadda ake gudanar da bikin kirsimeti a Yola.

Bishop Manza yace koyi da halayen Yesu Almasihu zai tamaka wajen nunawa juna kauna da kuma samun cigaban mabiya addinin na kirista a jiha dama kasa baki daya.

Manza ya kuma shawarci mabiya addinin kirista da suyi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen matsalar tsaro a fadin Najeriya baki daya.

Bishop har wayau ya kirayi mabiya addinin kirista da su kasance masu kaiwa makwabta dama ‘yan uwa ziyara a wannan lokaci domin samun cigaban kyautata dangantaka a tsakanin Jama a.

Labarai Makamanta