Adamawa: An Shawarci Iyaye Su Tarbiyyantar Da ‘Ya’yansu Karatun Alkur’ani

An kirayi iyaye musamman mata da su kasance masu nunawa ‘ya’yan su tarbiya da karatun Al qur’ani mai girma tun suna kanana domin samun cigaban karatun Al qur’ani dama tarbiya yadda ya kamata a tsakanin su.

Malama Aisha Adamu ce tayi wannan kira a lokacin bikin saukar karatun Al- qur’ani mai girma ƙarƙashin jagorancinta. Wanda aka gudanar a cikin garin Jimeta dake karamar hukumar Yola ta Arewa, fadar gwamatin jihar Adamawa.

Malama Aisha tace nunawa yara karatun Al qur’ani mai girma dama nuna musu tarbiya tun suna kanana ya na da matukan muhimmanci, wanda acewarta yaran baza su manta da abinda aka koya musu ba.

Ta kuma shawarci al’umma Musulmi da su kasance masu karatun Al-qur’ani mai girma a koda yaushe tare da gudanar da adduoi domin samun zaman lafiya a fadin kasar nan baki daya.

Harwa yau ta shawarci Dalibai da su kayi saukan da su kasance masu yin amfani da abinda aka koya musu domin samun cigaban karatun su yadda ya kamata.

Itama anata bangaren malama Farida Jibrin kuma tana daga cikin wadanda su kayi sauka kasancewarta matan aure kiran matan auren tayi da cewa basu makara ba su maida hankali wajen karatun addinin musulunci domin samun inganceccen tarbiya ga yara harma da cigaban addinin musulunci baki daya.

Ta kuma bayyana jin dadinta tare da godewa malamarta da ta yi hakurin karantar da ita har ta sauke, tare da yin fatan Allah madaukakin sarki ya bata damar cigaba da karantarwa.

Wasu daliban sun shaidawa muryar ‘yanci farin cikinsu tare da jin dadinsu dangane da wannan bikin sauka da aka shirya musu tare da kiran yara sa’aninsu su maida hankali wajen karatun Al qur ani mai girma.

An dai bata kyaututtuka Al qur’ani ga daliban da suka yi saukan da zummar kara musu karfin gwiwar cigaba da karatun Al qur’ani mai girma.

Sama da dalibai sha bakwai ne dai suka samu nasaran sukan karatun Al -qur’ani ani mai girma.

Labarai Makamanta