Adamawa: An Shawarci Iyaye Su Dage Wajen Ba ‘Ya’ya Tarbiyya

An kirayi iyaye da su kasance masu ba ‘ya’yan su inganceccen tarbiya domin ba yara tarbiyya na gari yana da matukan muhimmanci a tsakanin al’umma baki daya.

Mallam Muhammed Umar Zingin ne yayi wanna kira a lokacin da yake gabatar da nasiha a wajen taron kwamitin Women in Da’awa karo na farko a jihar Adamawa.

Muhammed Zingina yace iyaye su sani fa samun yara nagari suna daga cikin abin da mutum zai bari suna yiwa iyayensu addu’a suna raye ko sun mutu, don haka yana da mutukar muhimmanci iyaye su maida hankali a koda yaushe wajen ba yara tarbiya, musammanma a wannan lokaci da muke ciki na matsalar rayuwa da dai sauransu.

Zingina ya kuma kirayi yaran musamman ma matasa da su kasance masu yiwa iyayensu biyayya da kuma girmamasu a koda yaushe wanda a cewarsa haka zai sa su samu albarkar rayuwa da kuma cigaban lamurran su yadda ya kamata, ba tare da wata matsala ba.

Shima da yake jawabi a wajen taron shugaban majalisar addinin musulunci a jihar Adamawa kuma Shugaban taron Mallam GAMBO Jika yace shirya irin wannan taro yana da muhimmanci sannan ya jaddada kiransa ga iyaye da su kasance masu nunawa ‘ya’yan su hanyoyi da suka dace domin ganin sun samu ilimi da kuma sanin yadda zasu gudanar da rayuwarsu kamar yadda addinin musulunci ya tanata.

Ya kuma shawarci al’umma musulmai da su kasance tsintsiya madaurinki daya, domin samun cigaban addinin musulunci dama musulmai baki daya.

Tunda farko a jawabinta shugabar kwamitin Women in Da’awa a jihar Adamawa Hajiya Hannatu Usman tace dalilinsu na Shirya wannan taro dai shine nemo hanyoyi da za a warware matsalolin da ake samu na tarbiyar yara da kum yawan sake saken aure a tsakanin Al umma musulmai.

Don haka nema Hajiya Hannatu ta shawarci iyaye da su kasance masu sanin shige da ficen ‘ya’yan su da kuma sanin su wayene su ke Mu’amala dasu, wanda a cewar ta hakan zai taimaka wajen ganin yaran sun samu tarbiya nagari.

Itama anata bangaren Jami’ar watsa labaran kwamitin Hajiya Aisha Babadiya kiran iyayen tayi musammanma mata da su kasance masu tsoron Allah madaukakin sarki a zukatansu tare da ba yara ilimi addini dana zamani domin samun cigaban addinin musuluncin baki daya.

Hajiya Aisha ta kuma kirayi mahalarta taron da suyi amfani da abunda aka fada musu tare da kuma isarwa ga kananan hukumomi da suka fito domin ganin sun cimma nasaran abunda suke bukata na samun cigaban tarbiya.

Wasu mahalarta taron sun shaidawa muryan Yanci farin cikinsu dangane da shirya wanannan taro tare da yin alkawarin isarwa ga wadanda basu samu damar halartar taron ba.

Taron ya samu halartan wakilan kwamitin daga kananan hukumomin ashirin da daya dake fadin jihar Adamawa.

An kuma gudanar da addu’oi na musamman domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawar da dukkannin kalubalen tsaro a fadin Najeriya baki daya.

Labarai Makamanta