Adamawa: An Shawarci Iyaye Kan Ilimin ‘Ya’yansu

An kirayi iyaye da su kasance masu maida hankalinsu kan karatun yaransu yadda ya kamata domin ganin an samu cigaban ilimi mai ingaci.

Darsktan makarantar Firamare da Sakandare da Hight Islamic na Nurul Islam, dake cikin garin Jimeta a karamar hukumar Yola ta Arewa a jihar Adamawa, Mallam Abubakar Mega ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a Yola.

Malam Abubakar Mega yace maida hankali kan yaran zai taimaka wajen samarwa yaran ilimi dama basu tarbiya yadda ya kamata.

Ya kuma shawarci iyaye da su rinka tura yaran zuwa makarantu akan lokaci wanda acewarsa rashin zuwan yaran a makarantu akan lokaci yana bada gudumawa wajen durkushewar karatun yaran.

Saboda haka nema yace iyaye sun rinka binciken takardun yaran da zaran sun dawo daga makarantar domin hakan zai taimaka wajen samun wadataccen ilimi a tsakanin yaran.

Mallam Abbas Abubakar Malamine a makarantar ta Nurul Islam ya bayyana godiyarsa dangane da dawowa hutu da akayi tare da kiran iyaye da su baiwa malamai hadin kai domin ganin malamain sun cimma burinsu na karantar da yaran yadda ya kamata.

Wasu daliban makarantar sun shaidawa Muryar ‘yanci cewa sunji dadin dawowa hutu da suka yi tare da kiran iyaye da su hada kai da malamai domin samun cigaban karatunsu a koda yaushe.

Makwanni uku ne dai ɗaliban suka kwashe suna hutun farkon zango wanda kuma a ranan 10-1-2022 aka dawo hutun domin cigaba da karatun zango na biyu.

Labarai Makamanta