Adamawa: An Shawarci Iyaye Da Tura ‘Ya’yan Su Makaranta

An kira yi iyaye da su kasance masu mai da hankali wajen tura ‘ya’yan su Makarantu domin kawo saukin yawaitar Yaran da basu zuwa makaranta a tsakanin yara baki daya.

Shugaban Makarantar NAFAN ACADAMY Adamu Jingi wanda akafi sani da Maihange ne yayi wannan kira a lokacin bikin yayen daliban makarantar da ya gudana a harabar makarantar dake Jambutu a cikin karamar hukumar Yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Adamu yace baiwa yara ilimi abune da yake da matukan muhimmanci don haka bai kamata iyaye suyi sakaci da ‘ya’yan su ba, wajen basu ilimi mai inganci.

Ya kuma shawarci iyayen dama Malamai da su kasance masu sadaukar da kansu domin samun cigaban ilimin yaran yadda ya kamata.

Ya ja hankalin Malaman makarantar da su dauki daliban tamkar ‘ya’yan su, wanda a cewar sa hakan zai taimaka wajen baiwa yaran ilimi mai nagarta.

Shima anashi jawabi Malam Zakari Ali ya kirayi iyaye da su kasance masu baiwa Malamai hadin kai da goyon baya, su kuma rinka tura ‘ya’yansu makarantu akan lokaci domin malaman su samu kwarin gwiwa karantar da yaran yadda ya kamata.

An dai gudanar da raya rayen gargajiya da bada kaututtuka ga daliban da suka yi fice a sahin darasin kimiya tare da wasan kwaikwayo da dai sauransu.

Da suke bayani wasu da cikin wadanda aka yayen Aisha Muhammed da Auwal sun bayyana farin cikin su dangane da wannan yaye da akayi musu tare da godewa shugaban makarantar dama malamai bisa karantar da su da su kayi,sukace da yardan Allah madaukakin sarki zasu yi amfani da abinda aka koya musu ta hanyar da ya dace domin samun cigaban ilimi yadda ya kamata.

Related posts