Adamawa: An Shawarci Gwamnatoci Su Kara Kaimi A Harkar Noma

Domin ganin an samu cigaban harkokin noma a fadin Najeriya an kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da su kara kaimi wajen taimakawa manoma kasancewa noma ya zama babbar sana’a.

Alhaji Adamu Jingi ne yayi wannan kira a lokacin da yake zantawa da muryar yanci a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Alhaji Adamu ya yaba da yadda ake gudanar da harkokin noma a kimiyance musammanma yadda hukumar inganta fasahar tsirrai a Najeriya wato Agriculture Biotechnology ke inganta fasahar iri wanda acewarsa hakan cigabane kuma zai taimaka wajen bunkasa harkokin noma harma da samar da aikin yi a tsakanin matasa dake fadin kasan nan.

Saboda haka nema ya shawarci manoma da su tashi tsaye wajen rungumar harkokin noma domin samarwa kasan nan wadataccen abinci dama bunkasa tattalin arzikin kasan nan baki daya.

A cewar Alhaji Adamu dai an samu cigaba matuka a daminan bana duba da yadda al umma suka shiga daji domin gudanar da noma. Don haka ya kamata gwamnati ta cigaba da taimakawa manoma musamman ma wadanda ke yankunan karkara.

Ya zuwa yanzu dai manoma na cigaba da girbe anfanin gonakinsu lamarin da ake ganin za a samu saukin kayyayakin abinci a kasuwanni dake fadin kasan nan.

Labarai Makamanta