Adamawa: An Shawarci Gwamnatin Tarayya Da Ba Dillalan Mai Damar Shigo Mai

A wani mataki na magance karancin man fetur a fadin kasan nan baki daya. An sahawarci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta sakarma dillalain man fetur masu zaman kansu mara domin samun damar shigo da mai din.

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar dilalan man fetur mai zaman kanta a Najeriya IPMAN Alhaji Baba-Kano Jada ne yayi wanana kira a zantawarsa da Wakilinmu a Yola.

Alhaji Baba-Kano Jada yace mafita daga cikin matsalalolin karanci dama tsadar man fetur a fadin Najeriya ita ce a ba kamfanoni masu zaman kansu lasisin izinin shigo da man fetur da dangoginsa wanda a cewar sa hakan zai taimaka wajen samun saukin a bangaren man fetur a fadin Najeriya baki daya.

Ya kuma kira yi mambobin kungiyar da su kasance masu hadin kai domin samun cigaban kungiyar yadda ya kamata.

Baba-Kano ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su cigaba da yin addu’o’i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin matsalolin tsaro a fadin ƙasar baki daya.

Labarai Makamanta