Adamawa: An Shawarci Gwamnati Ta Ba Mata Mukaman Siyasa

An kirayi Gwamnati jihar Adamawa da ta sanya mata cikin harkokin gwamnati da ma siyasa domin matan su samu damar bada tasu gudumawar wajen samun cigaban jihar dama kasa baki daya.

Wata fitacciyar ‘yar siyasa kuma ‘yar jarida a jihar Adamawa wato Hajiya Laure Ahmed ce tayi wannan kira a lokacin da take zantawa da muryar ‘yanci a Yola.

Hajiya Laure tace gwamnati ta sani fa Mata suna bada muhimmiyar gudummawa wajen yin nasara a lokacin zabe don haka ya kamata gwamnati takasance tana ba mata damar don a dama dasu a harkokin siyasar jihar.

A cewar Hajiya Laure da sau da dama idan mata sun bada gudummawa wajen gangamin neman zabe amman da zaran anci zabe sai abarsu a baya.

Don haka nema take kira ga mata da su kasance masu hada kansu a koda yaushe da kuma shiga a dama dasu a cikin harkokin siyasa a fadin jihar ta Adamawa baki daya.

Ta kuma kirayi jam’iyun siyasa da su kasance masu ba mata mukaman da dama a cikin jam’iyun siyasa wanda a cewarta hakan zai taimaka wajen ba mata damar taka tasu rawan a harkokin siyasa.

Ta kuma kirayi ‘yan Najeriya da su cigaba da yin addu’o’i a koda yaushe domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen matsalar tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Labarai Makamanta