Adamawa: An Shawarci Gwamnati Da Sa Baki Kan Tsadar Fetur

A yayinda ake fuskantar matsalar karancin man fetur a jihar Adamawa an kirayi gwamnatin tarayya da ta sa baki domin ganin an samu saukin lamarin.

Alhaji Usman Abubakar wanda akafi sani da Manu Ngurore ne yayi wannan kira a zantawarsa da muryar yanci a Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Alhaji Manu Ngurore yace kiran ya zama wajibi in akayi la akari da yadda a yanzu manoma ke kokarin dawo da amfanin gonakainsu gida kwatsam sai ace ana samun karancin man fetur a fadin jahar wanda a cewarsa hakan bai dacebba.

Manu y akuma shaidawa gwamnatin ta tarayya da ta ja hankalin Dillalan man fetur din da su kaucewa duk abinda zai jefa talakawa cikin kuncin rayuwa.

Don haka ya kamata Gwamnati dama Dillalan mai din su tattauna su fahinci juna domin ganin lamarin ba kai ga kara farashin kayayyakin masarufi ba.

Harwayau Manu Ngurore ya kirayi Dillalan mai din da suyi wa Allah da manzonsa da sucigaba da gudanar da aiyukansu domin kaucewa shiga wahàlar rayuwa a tsakanin Al umma baki daya.

Yazuwa lakacin hada wannan rahoto dai gidajen mai da dama na rufe illa kalilan ne kawai za a iya ganin a buda suna sayar da mai din.

A lokacin muryar yan ci ta tuntubi jigo a kungiyar Dillalan man fetur din a jihohin Adamawa da Taraba Wato Alhaji Dahiru Buba yace dalilin da yasa aka fuskancin kàranci mai din yana da nasaba da rikice rikicen dake faruwa a kudancin Kasannan dama rashin kyau hanyoyin a wasu yankuna dake fadin kasan nan.

Labarai Makamanta