Adamawa: An Roki Gwamnatin Buhari Ta Janye Kudirin Cire Tallafin Fetur

An kira yi gwamnatin tarayya da ta yiwa Allah da manzonsa ta janye kudirinta na cire tallafin man fetur da tasa aniyar yi a shekara mai zuwa.

Wasu mazauna jihar Adamawa ne suka yi wannan kiran a zantawarsu da wakilinmu a Yola fadar gwamnatin jihar ta Adamawa.

Abdulrahman Musa mazaunin jihar Adamawa yace a gaskiya karin farashin mai din bazai haifar da ɗa mai ido ba, sai dai zai jefa talaka cikin kuncin rayuwa da kuma haifar da hàuhawan farashin kayayyaki a kasuwanni, harma dana sifiri.

Abdulrahman yace shugaban kasa fa da kansa yace bai kamata a sayar da man fetur Naira Hamsin a lita daya ba. Don haka ya kamata yayi la akari da irin halin da za a shiga in aka cire tallafin.

Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da sucigaba da yin adduo’i domin ganin an samu zaman lafiya a fadin kasan nan baki daya.

Shima anashi bangaren Muhammed Auwal Yakub yace ya kamata gwamnatin tarayya ta kasance tana tallafawa ne ba wai ta sanya al’umma cikin kuncin rayuwa ba.

Auwal yace a yanzu haka ma ana fama da tsadar rayuwa da suka hada dana kayan masarufi da dai sauransu. Saboda haka ya kamata gwamnti ta janye batun cire tallafi akan man fetur din.

Sannan ya shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu hada kansu a koda yaushe da kuma gudanar da ayyukan da zai kawo hadin kai, zaman lafiya dama cigaban kasan baki daya.

Labarai Makamanta