Adamawa: An Kona Jabun Magunguna Da Suka Haura Naira Miliyan 12

Cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya wato FMC yola tare da hadin gwiwar hukuman inganta magunguna da abinci ta kasa NAFDAC su tarwatsa tare da kona magunguna da kudinsu ya kai sama da Nera milyan goma sha biyu.

Da yake jawabi a yayin kona magungunan shugaban kwamitin kan lamarin dake FMC yola Ahmed Baba Usman yace wasu magungunan an karbesune a lokacin da suna daf da daina aiki a yayinda wasu kuma biyo bayan dokan kulle da akasa sakamokon cutar korona wanda a wancan lokacin an samu karancin marassa lafiya, saboda haka nema ba ayi amfani da wasu magungunan ba harsuka daina aiki.

Ya kara da cewa an dauki matakin haka ne domin ganin an samu cigaba tare da inganta lafiya al umma yadda ya kamata ba tare da wata matsalaba.

Yace an kona magungunan ne biyo bayan da hukumar inganta magunguna da abinci ta kasa NAFDAC tare da hukumar hanasha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato NDLEA suka ziyarci dakin ajiye magungunan cibiyar kiwol lafiya ta tarayya wato FMC Yola inda suka tanance tare da gano magunguna da auka daina aiki.

Shima anashi jawabi wakilin majalisar magunguna PCN a takaice Pharm Giwa A Emmanuel ya yabawa cibiyar kiwon lafiya ta tarayya FMC Yola bisa wannan na mijin kakari da sukayi na daukan matakin kona magungunan da suka daina akin wanda acewarsa hakan zai kawo cigaba dama samar da inganceccen kiwon lafiya a tsakanin al umma baki daya.

Da yake naahi jawabi wakilin NAFDAC Joshua Bitrus shima yace FMC tayi abunda ya dace kuma ya zama wajibi a yabamata bisa wannan kokari da cibiyar tayi na kona magungunan. Wanda hakan zai taimaka wajen yin amfani da ingantattun magungunan yadda ya kamata.

Labarai Makamanta

Leave a Reply