Adamawa: An Kirayi ‘Yan Najeriya Su Gaggauta Karbar Katin Zabe – Shugaban Gidauniyar Attarahu

An kirayi ‘yan Najeriya musammanma wadanda sukayi rijistan katin zabe da su gaggauta karba katin zabensu domin ganin an samu nasarar yin babban zaben shekara ta dubu biyu ta ashirin da uku mai zuwa.

Shugaban gidauniyar Attarahu dake jihar Adamawa Mallam Muktar Dayyib ne yayi wannan kira a zantawarsa da Wakilinmu a Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Malam Muktar Dayyib yace ya kamata mutane su sani karban katin zaben yana da matukar muhimmanci wanda hakan zai bada damar zabar shugabanni da suka cancanta in kuma har mutum bai da katin zabe zai zama dan kallo, saboda haka mutane kar suyi da wasa su tabbata sun karbi katin zabensu na din din din domin su samu damar yin zabe.

Da wannan ne yake shawartan ‘yan arewa da suma kada su bari a barsu a baya wajen mallakar katin zaben domin samun cigaban yankin na arewacin Najeriya.

Mallam Muktar ya kuma kirayi ‘yan siyasa da su yiwa Allah da manzonsa kada suyi amfani da siyasa wajen rarraba kan ‘yan kasan nan, don hakane ma ya shawarci ‘yan Najeriya musammanma matasa da kada su bari ayi amfani da su wajen yin dukkanin abinda zai kawo matsala a lokaci dama bayan zabe.

Harwayau Dayyib ya kirayi shugabanin kasan da su kasance masu yin duk abinda zai kawo hadin kai dama cigaban kasan nan baki daya.

Tare da kira da a cigaba da yi wa kasa addu’a dama shugabanni wanda a cewarsa shugaba addu’a ake musu, don haka mutane su nisanta kansu da zagin shugabanni.

Labarai Makamanta