An kirayi manoma da makiyaya a fadin Najeriya da su kasance masu hada kansu a koda yaushe domin ganin an samu cigaban harkokin noma dama zaman lafiya a fadin kasan nan baki daya.
Shugaban kungiyar manoma da sayar da kayayyakin noma wato AFGSAN na kasa Alhaji Haruna Fembeguwa ne yayi wannan kira a lokacin da kungiyar ta gudanar da taronta a Yola, fadar gwamnatin jihar Adamawa.
Alhaji Haruna yace Manoma da Makiyaya su sani fa dukkaninsu abu dayane don haka ya kamata su kasance masu kai zuciya nesa domin kaucewa tashin hankali a tsakaninsu.
Ya kuma kirayi manoma da kada su gaggauta sayar da abinda suka noma domin kaucewa shiga wahala a gaba. Tare da kiran daidaikun Jama a da su daina sayan abinci suna boyewa da niyyar sai yayi tsada kafin su sayar wanda a cewarsa Shari’a ta addini ma tayi hani da yin haka.
Don haka nema yake kiran gwamnatin tarayya dana jihohi da su maida hankali wajen adana kayayyakin abinci domin kaucewa tsadar kayan abinci.
Shugaban kungiyar ya kuma shawarci dukkanin masu ruwa da tsaki da suyi dukkanin mai yiwuwa domin ganin ba a samu hauhawan farashin kayan abinci ba a fadin Najeriya baki daya.
Fembeguwa ya kuma yi addu’ar Allah madaukakin sarki ya taimaka wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro dake ciwa kasar nan tuwo a kwarya.
You must log in to post a comment.