Adamawa: An Kama Mace Cikin Masu Garkuwa Da Mutane

A kokarinta na dakile dukkanin ayyukan ta’addanci a fadin jihar baki daya, rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa tana tsare da mutane uku ciki harda wata mace wadanda ake zargi da yin garkuwa da wani yaro ɗan shekaru Tara da haihuwa.

Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, wanda kuma aka rabawa manema labarai a Yola.

Sanarwar tace bayan kama wadanda ake zargin an kuma ceto yaron da suka yi garkuwa dashi biyo bayan samame da aka kai a maboyar ‘yan Bindigan.

Wadanda aka kaman dai sun hada
da Abdullahi Saleh dan shekaru ashirin da biyar wanda ya fito daga unguwar hausawa a cikin karamar hukumar Jos ta arewa, da Ayuba Tanko dan shekaru ashirin da bakwai shi kuma yafitone daga jahar Bauchi sai kuma Victoria Samaila ‘yar shekaru sha takwas tana zaune ne a Sanger a cikin karamar hukumar Girei a jihar Adamawa.

Anyi nasarar kama wadanda ake zargin ne a yayin da suke jiran a kawo musu kudin fansa na naira Milyan 30 wanda hakan yayi sanadiyyar cika hannu dasu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa CP Muhammed Ahmed Barde ya tabbatarwa al’ummar jihar Adamawa cewa rundunar a shirye take ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a, don haka akwai bukatar Al’umma su kasance masu taimakawa rundunar da bayanai da zai taimakawa wajen dakile ayyukan ta’addanci a jihar

Yanzu haka dai ana cigaba da bincike kan wadanda ake zargi wanda a cewar kwamishinan ‘yan sandan da zarar an kammala bincike za a gurfanar dasu a gaban kotu domin su fuskanci Shari’a,

Labarai Makamanta