Adamawa: An Kalubalanci ‘Yan Sanda Da Kara Kaimi

Rahotannin dake shigo mana daga Yola babban birnin jihar Adamawa na bayyana cewar an kirayi Jami’an ‘yan Sanda da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukan su domin ganin an samu cigaban zaman lafiya da dakile ayyukan ta’ddanci baki daya a jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Adamawa CP S.K Akande ne yayi wannan kira a lokàcin da ake gudanar da bikin ƙarawa Jami’an ‘yan sandan girma wanda aka gudanar a Yola.

Kwamishinan yace dole ne ‘yan sandan su jajirce wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata domin kare rayuka da dukiyoyin Al’umma baki daya.

Ya kuma kirayi wadanda aka kara musu girman da su maida hankali wajen gudanar da ayyukan su domin a cewarsa mai da hankali wajen aiki zai taimaka wajen samun karin girma yadda ya kamata.

Wasu daga cikin wadanda suka samu karin girman dai sun shaidawa wakilinmu farin cikinsu da kuma jin dadinsu dangane da wannan karin girma da suka samu tare da tabbatar da cewa zasu yi dukkanin abinda ya dace domin samun cigaban ayyukan ‘Yan sanda.

Akalla jami’an ‘yan sanda ɗari ne da suka samu karin girman ciki harda kakakin rundunan yan sandan jihar Suleiman Yahaya Nguroje wato ya samu matsayi daga DSP zuwa SP.

Har wayau rundunan ‘yan Sandan jahar ta samu nasaran kama mutane goma sha uku bisa zarginsu da aikata lafuka daban daban a sassa daban daban dake fadin jihar Adamawa.

Da yake gabatarwa manema labarai wadanda ake zargin CSP Ahmed D Gombi a madadin Kwamishinan ‘yan sandan jahar yace sun samu nasaran kama mutanen ne tare da hadin gwiwar mafarauta biyo bayan samame da aka kai a maboyansu a wurare daban daban.

Rundunan ‘yan sandan dai tace da zaran ta kammala bincike akansu za a gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci Shari’a.

Labarai Makamanta