Adamawa: An Kalubalanci ‘Yan Jarida Da Yin Aiki Bisa Tsari

An kirayi ‘yan jaridu a jihar Adamawa da su kasance masu gudanar da ayyukan su kamar yadda doka ta tanada domin samun cigaban aikin yadda ya kamata.

Shugaban kungiyar yan jaridu na jihar Adamawa Kwamared Ishyaku Donald Dedn ne yayi wannan kira a lokacin da yake jawabi a wurin Babban taron kungiyar da ta gudanar a sakatariyar kungiyar dake Yola.

Donald Dedan yace ‘yan jaridu suna da rawa da zasu iya takawa wajen hadin kan al umma. Zaman lafiya harma da cigaba jihar dama kasa baki daya.

Ishyaku ya kuma shawarci membobin kungiyar da su kasance masu gudanar da ayyukan su bil hakki da gaskiya, tare kuma da kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin al’umma.

Shima anashi jawabi Mataimakin Shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa shiyar yankin arewa maso Gabas Mr Zare Baba shima kiran membobin kungiyar yayi da su kasance masu hada kansu a koda yaushe da kuma yin duk abinda ya dace domin samun cigaban kungiyar yadda ya kama.

Kungiyar yan jaridun dai tayi amfani da wannan dama wajen kiran ‘yan Najeriya da su kasance masuyin addu’oi a koda yaushe domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Taron dai ya samu halartan daukacin yan jaridu dake fadin jihar ta Adamawa.

Labarai Makamanta