Adamawa: An Kalubalanci Soji Da Kara Kaimi A Harkar Tsaro

An kirayi rundunan sojojin Najeriya da su kara kaimi wajen magance kalubalen tsaro da yake ciwa gwamnatin kasan nan tuwo a kwarya.

Gwamnan jihar Adamawa ne Ahmadu Fintiri yayi wannan kira a lokacin da yake zantawa da manema labarai a lokacin bikin tunawa da mazan jiya wanda aka gudanar a dandalin Mahmudu Ribadau dake Yola.

Gwamnan yace sojoji sun taka rawan ganin wajen kare Martaban kasan nan saboda hakane ma yake shawartan sojojin da su kara damara domin Samar da zaman lafiya a fadin Najeriya baki daya.

Bikin ya samu halartan Kwamandan rundunan bataliya ta Ashirin da uku dake nan Yola, tare da manyan jami’an soji dama wakilin kwamishinan yan sanda da dai sauransu.

Gwamnan tare da mai martaba Lamido Adamawa Dr Muhammed Barkindo Aliyu Mustafa da manyan Jami’an soji sun jera furanni domin tunawa da tsaffin sojojin.

Shugaban kungiyar tsoffin sajojin a jihar Adamawa Muhammed Ali ya godewa Gwamnan bisa goyon baya da yake baiwa tsoffin sojojin, tare da kira a cigaba da taimakawa tsoffin sojojin Musamman ma matan sojojin da suka mutu a bakin daga.

Suma matan sojojin da suka mutu ba abarsu a bayaba sun halarci bikin tare da sojojin da suka samu rauni a wurin yaki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply