Adamawa: An Haramta Ayyukan Mafarauta


Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a ranar Litinin ya haramtawa kungiyar kwararrun mafarauta ta Najeriya gudanar da ayyukanta a fadin kananan hukumomin jihar 21, biyo bayan rahotannin amfani da karfin iko.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai taken ‘Gwamnatin Jihar Adamawa ta haramtawa kungiyar mafarauta yin aikinta’ mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Humwashi Wonosikou.

Gwamnan ya bayyana cewa an samu rahotannin cin zarafi da rashin kula da cibiyoyin gargajiya da hukumomin tsaro da mafarauta ke yi, musamman a kananan hukumomi biyar da suka hada da Demsa, Numan, Lamurde, Guyuk, da Shelleng.

“Ayyukan kungiyar a kananan hukumomi biyar sun zama abin damuwa da rashin tsaro, maimakon tsaron da aka samar,” in ji Fintiri.

Gwamnan ya kara da cewa ayyukan mafarauta na iya haifar da matsala tare da dagula al’umma. Don haka ya kamata su daina yin duk wani aiki da sunan samar da tsaro ga jama’a.

An rawaito cewa ya kuma umurci jami’an tsaro da su tabbatar da cewa haramtacciyar kungiyar ta bi wannan mataki yana mai cewa, “Ina kira ga jami’an tsaro da na gargajiya dasu hada kai don tabbatar da cewa an wanzar da zaman lafiya a fadin jihar kafin lokacin da kuma bayan bukukuwan Yuletide da kuma bayan bukukuwan sabuwar shekara”.

Labarai Makamanta