Adamawa: An Gwangwaje Daliban Makarantar Gongoshi Da Kyaututtuka

Domin ganin an samu cigaban ilimi a tsakanin yara dama al’umma ne dai an taimakawa ɗaliban makarantar Firamare dake garin Gongoshi 3 a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

Taimakon dai ya gudanane karkashin jagorancin Alhaji Usman Abubakar Ngurore wanda akafi sani da Manu Ngurore domin ganin daliban sun samu damar yin karatu cikin tsanaki da nutsuwa.

A jawabinsa Shehu Ahmed yaja hankalin mazauna garin na Gongoshi 3 da su kasance masu taimakawa kansu a koda yaushe wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen bunkasa ilimin daliban yadda ya kamata ba tare da wata matsalaba.

Ya kuma kira yi Matasan garin da suma su hada kansu kuma su kasance masu bada gudumawa wajen cigaban garin na Gongoshi baki daya.

Shima a jawabinsa Alhaji Usman Abubakar kiran iyayen yaran yayi da su taimaka su rinka tura yaransu a makaratar a koda yaushe domin ganin an samu nasara wajen baiwa yaran ilimi mai inganci a tsakanin daliban yadda ya kamata.

Suma daliban ya shawarce su da su maida hankali wajen yin karatu wanda a cewarsa hakan zai basu damar yin karatunsu ba tare da wata matsalaba.

Jika Ahmed kansila dake wakiltan yanki ya nuna jin dadinsa dangane da wannan taimako da akayi tare da kiran masu hannu da shuni da suyi koyi da Alhaji Usman Abubakar ta wajen gudanar da irin wadannan taimako domin samun cigaban al’umma baki daya.

Anashi ɓangaren shugaban makarantar firamare Muhammed Julde shima bayyana farin cikinsa yayi dangane da wannan taimako da aka kawowa makarantar.

Abubuwa da aka taimaka da su dai sun hada da takardun rubutu, uniform, Biro da dai sauransu, sama da ɗalibai dari biyi da hamsin ne dai zasu ci gajiyar taimakon.

Labarai Makamanta