Adamawa: An Damke WandaYa Kashe Matarshi Ta Hanyar Daba Mata Wuka

A yanzu haka rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa tana tsare da wani magidanci mai suna Muhammed Alfa dan shekaru hamsin da bakwai da haihuwa wanda yake zaune a cikin kauyen Lande B a karamar hukumar Gombi dake bisa zarginsa da daɓawa tsohuwar matarsa wuka wanda kuma yayi sanadiyar mutuwarta.

Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Yola.

Sanarwa ta bayyana cewa matar mai suna Hamsatu ta gamu da ajalintane biyo bayan takaddama da ta shiga tsakaninta da tsohon mijin nata akan murfin kofa da tayi kokarin cirewa domin ta sa a dakin da ta koma bayan ya saketa. Inda shi kuma yace hakan ba zai yuyuba, a dalilin haka ne sai ya daba mata wuka a wuya, an dai garzaya da ita zuwa asibitin amma rai yayi halinsa.

Ofishin ‘yan sandan karamar hukumar Gombi ne suka samu nasaran cafke magidancin biyo bayan da mai unguwar Lande B wato Jauro Babangida Boka ya shaidawa ofishin yan sandan aukuwar lamarin.

Don haka nema Kwamishinan ‘yan sanda jihar Adamawa CP Muhammed Ahmed Barde ya bada umurnin gudanar da bincike dangane da lamarin tare da kiran al’ummar jahar ta Adamawa da su cigaba da taimakawa ‘yan sanda da wasu bayanai da zai taimaka wajen kama masu aikata laifi a tsakanin Jama’a.

CP Muhammed Barde ya gargadi Al’umma da su daina daukan doka a hannunsu domin runduna ‘yan sandan ba za ta lamunce da haka ba.

Har wayau kwamishinan ‘yan sandan yace da zaran an kammala binciken kan wanda ake zargin za a gurfanar dashi a gaban kotu domin ya fuskanci shariya.

Labarai Makamanta