Adamawa: An Damke Wadanda Suka Yi Garkuwa Da ‘Dan Shekara 8

A yanzu haka rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi dayi garkuwa da wani yaro mai suna Jafaru Hamisu dan shekaru takwas da ahifuwa tare da neman kudin fansa akan naira milyon biyar.

Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a yola.

Sanarwan dai ta baiyana cewa an samu nasaran cafke wadanda ake zargin biyo bayan da wani mai suna Alhaji Hamisu Sule wanda yake zaune a chigari a cikin karamar hukumar Fufore dake jahar Adamawa ya sanar da batan yaronsa mai suna jafaru.

Wadanda ake zargin dai sun hada da Junàidu Muhammed dan shekaru aahirin da takwas da haifuwa sai Aliyu Alhaji Aliyu shikuma yana da shekaru Hamsin da biyar da haifuwa wadanda suka fito daga karamar hukumar Lambata a jahar neja.

Bincike ya nuna cewa mutanen biyu dai suna zaunene a cikin garin chigari da sunan manomane kwatsam kawai sai sukayi garkuwa yaron.

Ya zuwa yanzu dai kwamishinan yan sandan jahar Adamawa C P Ahmed Muhammed Barde ya bada umurnin bincike akansu kuma ya ce da zaran ankammala bincike za a gabatar da su a gaban kotu domin su fukanci Shari a.

Labarai Makamanta