Adamawa: An Damke Gwanayen Barayi Uku

Rundunan ‘yan sanda a jihar Adamawa ta cika hanu da wasu mutane uku da ake zargi da kwarewa wajen yin fashi da zaran sun ga mutum ya fito daga banki ko kuma ya sayar da shanunsa.

Kakakin rundunan yan sandan jihar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Yola wanda aka rabawa manema labarai.

D S P Suleiman yace an samu nasarar kama wadanda ake zarginne biyo bayan wani sintiri da Jami’an ‘yan sandan keyi baya rundunar ta samu bayanan sirri daga wurin jama a, wanda hakan yasa aka tura Jami’an ‘yan sandan domin gano gaskiyar lamarin.

DSP Yahaya yace yanzu haka kwamishinan yan sandan jihar Adamawa CP Muhammed Ahmed ya bada umurnin gudanar da bincike kan wadanda ake zargi kuma ya tabbatar da cewa da zaran sun kammala bincike za a gurfanar dasu gaban Shari’a.

An dai gano dubu ashirin da shida tare da masta ki da katin cire kudi, wayoyin hanu da dai sauransu, a hannun su.

Don haka nema kakakin rundunan yan sandan ke kira ga al’ummar jihar da su kasance masu taimakawa hukumomin tsaro da wasu bayanan sirri wanda hakan zai ba hukumomin tsaron kwarin gwiwa wajen dakile ayyukan ta’addanci a tsakanin al’umma baki daya.

Labarai Makamanta