Adamawa: An Ceto Uwa Da ‘Yarta Daga Hannun ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar Rundunar ‘yan Sandan jihar tayi nasaran ceto wata uwa ma shayarwa wadda akayi garkuwa da ita tare da ‘yarta ‘yar shekaru biyu da haihuwa.

Kakakin rundunan ‘yan Sandan jihar DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a birnin Yola.

DSP Suleiman Yahaya yace ofishin Rundunar dake karamar hukumar Gombi a jahar Adamawa tare da hadin gwiwar mafarauta ne aka samu nasaran ceto matar mai suna Jimrewa Las. Da ‘yarta mai suna Grace Las a wani samame da aka kai a maboyar masu yin garkuwa da mutanen, inda akayi dauki ba dadi da ‘yan bindigan har aka ci nasara a kansu, inda suka ranta ana kare tare da raunin harbi bindiga a jikinsu.

Har wayau rundunan tayi nasaran kama mutane uku da ake zargi da yin garkuwa, wani mai suna Ali Yusuf wanda ke kauyen kadarbu a karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa harma sun nemi kudin fansa na naira Milyan biyu da dubu dari biyar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Adamawa CP Muhammed Ahmed ya tabbatarwa gwamnatin jahar Adamawa da ma al’ummar jihar cewa rundunan a shirye take domin ganin an kawo karshen ta’addanci a fadin jihar baki daya.

Don haka nema kwamishinan ya kirayi jama a da su kasance masu taimakawa rundunan ‘yan sandan ta hanyar basu hadin kai da goyon baya domin ganin ta samu nasaran kawar da aikata laifuka a fadin jahar.

Labarai Makamanta