Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Adamawa: An Bukaci Gwamnati Da Ta Aiwatar Da Dokar Kare Hakkin Yara

An kirayi gwamnatin jihar Adamawa da ta kafa kwamitin da zai aiwatar da dokan kare hakkin yara a fadin jihar baki daya.

Kodinatan kungiyar kare hakkin yara a jihar Adamawa Kwamared Sunday Kadiri ne ya yi wannan kira a zantawarsa da Wakilinmu a Yola fadar gwamnatin jihar ta Adamawa.

Mr Sunday yace kafa kwamitin zai taimaka gaya wajen aiwatar da dokar a tsakanin al’umma don haka nema yake jaddada kiransa ga gwamnatin da ta gaggauta kafa kwamitin domin ganin an samu cigaba wajen kare hakkin yara a fadin jihar baki daya.

Kadiri ya kuma kirayi iyaye dama masu ruwa da tsaki da su bada hadin kai da goyon baya domin ganin an samu damar aiwatar da dokan kare hakkin yaran yadda ya kamata.

Harwayau Kwamared Sunday ya yi gargadin cewa a daina cin zarafin yara don kuwa akwai doka da zata yi aiki kan duk wanda aka kama da cin zarafin yara.

Ya kuma godewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da majalisar dokokin jihar tare da British council, Malala fund da dai sauransu bisa namijin kokari da suka yi na ganin cewa an samar da dokar da zata kare hakkin yara a fadin jihar ta Adamawa.

Shima anashi bangaren sakataren kungiyar Malam Yahay Ahmed Iya kiran sarakunan gargajiya yayi da su kasance masu bada hadin kai da goyon baya kasancewa suna da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa wajen kare hakkin yara.

A cewarsa da akwai kyakkyawar alaka a tsakaninsu da hukumomin tsaro don zasu yi dukkanin abinda suka dace domin ganin an kawo karshen cin zarafin yara.

A kwanan nan ne dai gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya sanya hannu kan kudirin doka kare hakkin yara bayan da majalisar dokokin jihar ta amince dashi kuma ta mikawa gwamnan domin ya sanya hannu.

Exit mobile version