Adadin Mutanen Da Ake Kashewa A Najeriya Ya Ragu Matuka – Rahoto

A wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan sha’anin tsaro a Najeriya ya fitar, ya ce an samu raguwar kashi 39 cikin dari a watan Yuli na yawan mutanen da ake kashewa a ƙasar, idan aka kwatanta da yawan waɗanda suka mutu a watan Yunin da ya gabata.

Masana harkar tsaro na ganin cewa wasu sauye-sauye da ake samu a ɓangaren na tsaro sun fara tasiri wajen rage mutanen da suke rasa rayukansu sanadiyyar tashe-tashen hankula a kasar.

Najeriya na fama da matsalar tsaro musamman a arewacin kasar, abinda ke haifar da rasa rayuka da tagayyara al’umma a kusan kowace rana.

Malam Kabiru Adamu shine jami’in hulda da jama’a na kamfanin, a zantawar su da gidan rediyon BBC Hausa, ya bayyana cewar wannan cigaba da aka samu ya biyo bayan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka ne karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ƙara da cewar a wani zama da Buhari ya yi da shugabanni tsaro a kwanakin baya, abubuwa sun sauya matuka inda aka ga an zafafa kai hare hare a maboyar ‘yan Ta’addan wanda hakan ya taimaka gaya.

Hakazalika ya bayyana kalaman da mai ba shugaban ƙasa shawara akan harkokin tsaro Babagana Mungono ya yi na cewar ya kamata a samu hadin kai tsakanin bangarorin tsaro a kasar da cewar kiran ya yi tasiri sosai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply