Abuja – Motace Ta Banke Dan Jaridar Vanguard – ‘Yan Sanda

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa wani direban mota ne ya kashe dan jaridar Vanguard, Tordue Henry Salem, wanda aka tsinci gawarsa a ranar Alhamis, a yashe.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan kasar, CP Frank Mba, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 12 ga watan Nuwamba, yayin da yake gurfanar da direban a harabar rundunar IRT da ke Guzape, Abuja.

Mba ya bayyana cewa an gano gawar Salem ne a babban asibitin Wuse. A yayin gurfanar da shi, direban mai suna Itoro ya bayyana cewa ya banke dan jaridar ne a yankin Mabushi a ranar 13 ga watan Oktoba, sannan sai ya tsere.

A baya mun kawo cewa, an gano gawar dan jaridar Vanguard da ke dakko rahotanni daga Majalisar Tarayya, kimanin wata daya dabacewarsa. An yi wa Tordue Salem ganin karshe da ransa ne a kusa da gidan man Total da ke kusa da hedkwatar rundunar yan sanda ta Abuja a ranar 13 ga watan Oktoban 2021.

An kama wasu mutane ciki har da wani Prince Enyenihi da ake zargi da hannu a bacewarsa.

Labarai Makamanta