Abin Kunya Ne Yadda Zabukan Fidda Gwani Suka Kasance – Jonathan

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi Allah wadai da zaben fidda gwani da jam’iyyu ke yi a kasar nan.

Da yake bayani a Abuja a ranar Alhamis wajen kaddamar da wani littafi mai suna “Political Party Governance” wanda Dr Mohammed Wakili tsohon ministan lantarki a lokacin Jonatha ya rubuta, ya ce abin kunya ne ka ba wakilai kudi su zabe ka, bayan ka fadi kuma ka ce su mayar maka da kudinka.

Ya kara da cewa “Duka zabukan da ake yi a fadin kasar na fidda gwani shiririta ne. Ba haka ake gudanar da zabukan ba.”

Labarai Makamanta