Abdul-Samad Isiyaka Rabi’u Ya Bada Tallafin Biliyan Guda Ga Jami’a

Shugaban Kamfanin BUA, Alhaji Abdul-samad Rabi’u ya bada kyautar zunzurutun kuɗi har Naira biliyan guda ga jami’ar Ibadan (UI) domin gyaran jami’ar da inganta harkokin ta yadda ya kamata.

Alhaji Rabi’u ya bada kyautar ne a wata ziyara da yakai ofishin muƙaddashin shugaban jami’ar, Prof. Adebola Babatunde Ekanola, ranar Alhamis.

Abdul-Samad Rabiu, wanda daraktan alaƙar gwamnati a kamfanin BUA, Dr. Aliyu Idi Hong, ya wakilta yace an baiwa jami’ar wannan kyautar kuɗinne saboda yadda take gudanar da ayyukanta masu kyau.

A jawabin da yayi lokacin amsar tallafin, muƙaddashin shugaban jami’ar ya godewa gidauniyar Abdul-Samad Rabiu (ASR) da gaba ɗaya tawagar Kamfanin BUA bisa wannan huɓɓasa da suka yi.

Prof. Ekanola ya ƙara da cewa hukumar makarantar zata yi amfani da wannan tallafin wajen bada horo ga ɗalibanta domin su zama waɗanda za’a yi alfahari da a duniya.

Labarai Makamanta