Zanga-Zangar Tsige Ganduje Ta Barke A Hedkwatar APC
Wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a hedikwatar Jam’iyyar APC mai mulki da ke Abuja, suna neman shugabantan riko na kasa, Abdullahi Ganduje, ya sauka daga mukaminsa. Masu zanga-zangar suna kuma kira ga Shugaba Bola Tinubu da Sakataren Gwamnati, George Akume, su duba yiwuwar mayar da shugabancin jam’iyyar...