A Shirye Nake Na Yi Sulhu Da Kwankwaso – Ganduje

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje ya ce a shirye ya ke da ya gyara alakar da ke tsakaninsu da sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a koma kamar yadda ake a baya.

A wata tattaunawa wadda Rediyo France ta yi da gwamnan ya kwatanta rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu da Kwankwaso tsakanin sabani, amma komai zai iya daidaita.

“Kun san akwai masu hura wa rigima wuta. Don haka yanzu haka muna kokarin ganin mun dakatar da su tare da gyara alakarmu da zaman amana da lumana kamar yadda muke a baya.

“Irin wannan fadan ko saɓanin ya dade yana faruwa ba sabon abu bane kuma zai wuce. Kowa ya san sulhu ya fi komai zama alheri. Muna fatan Ubangiji zai taimaki masu kokarin shirya mu.

“A wurinmu kuwa, a shirye muke da mu hada kai don shiryawa. Ba wai mun ki bane. Akwai masu rura wuta ko ta ina, amma na ce duk abinda aka yi amfani da hankali wirin aiwatar da shi ina ganin zai wuce.”

A ranar Talata, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya je yiwa Sanata Rabi’u Kwankwaso ta’aziyya, a gidansa da ke Bompai, layin Miller akan rasuwar dan uwansa, Inuwa Musa Kwankwaso.

Labarai Makamanta