A Shirye Muke Mu Tallafi Najeriya – Rasha

Rahotanni dake shigo mana daga ƙasar Rasha na bayyana cewar Ma’aikatar Ilimi ta kasar ta shaida wa ‘yan Najeriya cewa a shirye ta ke ta basu guraben karatu idan suna sha’awar cigaba da karatunsu a kasar.

Mikhail L. Bogdanov, Shugaban Rasha na Kasashen Tsakiya da Afirka kuma mataimakin Ministan Harkokin Kasashen Waje na Rasha ne ya sanar da hakan.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da jakadan Najeriya a Rasha, Abdullahi Shehu, kamar yadda gidan Talabijin Channels TV ya ruwaito.

Bogdanov, wanda ya tarbi jakadan na Najeriya a ofishinsa, ya tabbatarwa Shehu cewa Rasha za ta bada taimakon da ya dace don tabbatar da tsaro da walwalar daliban Najeriya mazauna Rasha.

Hakan na zuwa ne yayin da rikici ya barke tsakanin Rasha da Ukraine da ya yi sanadin mutane da dama suna tserewa daga Ukraine. Ya kara da bawa jakadan Najeriyan tabbacin cewa Rasha ta dauki Najeriya a matsayin kasa mai muhimmanci a Africa kuma za ta cigaba da karfafa dankon zumunci da ita.

A martaninsa, Farfesa Abdullahi Shehu ya mika godiyarsa ga Gwamnatin kasar Rasha kan damuwar da ta nuna ga halin da yan Najeriya ke ciki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply