A Gaggauta Ɗaukar Mataki Kan Masu Kisan Fulani A Kudanci – Miyyeti Allah

Ɗaya daga cikin ƙungiyoyin Fulani makiyaya a Najeriya, Miyetti Allah Kautal Hore ta buƙaci hukumomin tsaron kasar su hukunta ƴan bindigar da ke kashe Fulani makiyaya a yankin Kudu maso Gabashin kasar.

Mai magana da yawun ƙungiyar Saleh Alhassan cikin tattaunawar da ya yi da jaridar The Punch, ya bayyana haka a matsayin martani ga kisan ɗaya daga cikin kwamandojin haramtacciyar ƙungiyar IPOB mai fafutukar kafa ƙasar Biafra da jami’an tsaro suka yi ranar Asabar.

Tun farko jaridar ta rawaito yan sanda da takwarorinsu sojoji da jami’an hukumar farin kaya sun halaka jagoran IPOB mai suna Ikonso da wasu mutum shida a jihar Imo.

Sai dai mai magana da yawun kungiyar Miyetti Allah ya yaba wa jami’an tsaro inda “ya nemi su ƙara azama wajen murkushe duk wasu masu tada zaune tsaye a Najeriya”.

Ya ce kimanin Fulani 50 aka kashe a Kudu maso Gabashin kasar cikin wata daya da ya gabata.

Labarai Makamanta