A Gaban Idona Aka Zare Ran Kanina – Dangote

Daga karshe mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya magantu a kan rasuwar kaninsa, Alhaji Sani Dangote.

Marigayin wanda ya kasance mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya rasu a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba, a kasar Amurka bayan ya yi jinya.

Da ya tarbi jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Kano, a ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, Dangote ya ce mahaifiyarsu da yaran Sani na a wajen da aka dauki ran marigayin.

Ya ce ya fi masu radadi a lokacin da likitoci suka fada masu cewa dan uwansa na da kimanin awa daya da yayi masa saura kafin ya mutu, Daily Trust ta rahoto.

Dangote ya ce: “Yana da radadi saboda ya mutu a gabana, a gaban mahaifiyarmu da kuma yara.”

Ya ce shi da kansa saida zuciyarsa tayi rauni ganin ran dan uwansa yana fita daga jikinsa ta na’ura a asibitin.

Ya yi godiya ga Tinubu a kan ziyarar da ya kai masa, yana mai cewa ya ji dadin dangantakar yan uwantaka da ke tsakaninsa da ahlin Tinubu na tsawon lokaci.

Dangote ya ce rashin tabbas da ke tattare da mutuwa shi ne dalilin da ya sa ake so a kullum mutum ya dunga yin aikin alkhairi.

Ya kara da cewa:
“Yadda mutane ke ta zuwa abu ne mai matukar ban mamaki.
“Ziyarar zai taimaka mana wajen rage radadin musamman gareni saboda mun taso tare.
“Ya yi mana zafi sosai a lokacin da suka gaya mana cewa zai mutu nan da ‘yan sa’o’i kuma dole ne mu kalli yadda numfashinsa na karshe ya fita.”

A sakon ta’aziyyarsa, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin dan Lagas kuma babban dan Najeriya.

Tinubu ya kuma bayyana cewa kudi baya siyan rai kuma babu abun da mutum zai iya yi idan lokaci yayi, rahoton Vanguard.

Ya yi kira ga iyalan marigayin da su dauki hakuri da ci gaba da yi masa addu’an samun dacewa.

Labarai Makamanta