A Ɓoye Nake Soyayyata – Rahama Sadau

Fitacciyar Tauraruwar Masana’antar Hausa Fim ta Kannywood, Rahama Sadau ta ce ba ta yi imani da bayyana soyayya da babbar murya ba, kamar yadda ta fi so ta sanya rayuwar soyayyar ta zama sirri a boye daga ita sai masoyinta.

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ta yada a shafinta na Twitter, @Rahma_sadau ranar Juma’a.

Ban yi imani da bayyana soyayya a fili ba, na fi son ta sirri saboda ni rayuwata cikin sirri nake tafiyar da ita.

“To dai, na fi son kiyaye soyayyata cikin shirri. Abu daya ne duniya ta san mu dashi bangaren nishaɗantarwa, amma ɓangaren soyayyata sirri ne ni kaɗai na santa sai masoyina wanda nake fatan zama uwar ‘ya’yan shi.

Sadau, wacce ta yi suna a karshen shekarar 2013 bayan ta shiga masana’antar finafinai ta Kannywood tare da fim dinta na farko Gani ga Wane, ta kara da cewa “Ban yi imani da soyayya a bayyane da babbar murya ba. Ina son sirri na tsakani na da masoyina kawai.

Labarai Makamanta