Ban Da Wani Shiri Na Yin Tuggu Ga Tinubu – Gwamnan Babban Banki

An ruwaito wata kafar yada labarai ta bayyana cewa babban bankin ya saki naira miliyan 500 na cikin sabbin takardun kudi domin bai wa dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour a Legas, Mista Gbadebo Rhodes-Vivour nasara kan sauran manyan jam’iyyu biyu a zaben gwamnan da za a yi ranar Asabar mai zuwa. Amma a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, mukaddashin Daraktan Sadarwa na CBN, Isa Abdulmumin, ya ce Emefiele “bai taba ganawa ko ma magana da Mista Gbadebo Rhodes Vivour ba”. Da yake ambato wasu majiyoyi…

Cigaba Da Karantawa

Babban Banki Ya Amince A Cigaba Da Amfani Da Tsoffin Kudi

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce a yanzu al’ummar kasar za su iya ci gaba da amfanin da tsofaffin takardun kudi na naira 200, da 500 da kuma 1,000. A wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Litinin da daddare, wadda ta samu sa hannun mukaddashin daraktan yada labarai na bankin, Isa AbdulMumin, bankin ya ce ya yi hakan ne domin jadadda bin doka irin ta gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Sanarwar ta ce, “Bisa yin biyayya ga halayyar girmama shari’a ta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, da kuma na ayyukan Babban…

Cigaba Da Karantawa

Karancin Kudi: Ban Umarci Babban Banki Da Kin Bin Umarnin Kotu Ba – Buhari

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar shugaban kasa ta ce Babban Bankin ƙasar ba shi da wani dalili na ƙin bin umarnin Kotun Ƙoli kan sabbin takardun kuɗi don fakewa da sunan jiran umarni daga Shugaba Muhammadu Buhari. Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa inda ya ce Shugaban ƙasar bai umarci atoni janar na ƙasa, Abubakar Malami da Gwamnan CBN, Godwin Emiefele su ƙi martaba umarnin kotu ba da ya shafi gwamnati…

Cigaba Da Karantawa