Al’ummar karamar hukumar kudan dake jihar Kaduna, sun bayyana Sanata Uba Sani a matsayin Dan takarar da yafi Kowane Dan takarar cancantar zama gwamna jihar Kaduna. Bayanin haka ya fito ne daga shugaban karamar hukumar kudan Honarable Shu’aibu Bawa Jaja, a yayin da yake jawabi a dandamalin taron magoya bayan jam’iyyar APC da suka tarbi Sanata Uba Sani a filin wasa na kudan. Bawa Jaja ya ce, idan za’a yi maganar kwarewa da cancanta ne, to kaf babu tamkar Uba Sani, domin shi yayi angani a kasa, ba kamar sauran…
Cigaba Da KarantawaDay: January 27, 2023
TARABA: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Iyalai 8 Na Basarake A Jalingo
BASHIR ADAMU, JALINGO Rahotannin dake zuwa mana yanzu daga Jalingo, fadan Gwamnatin Jihar Taraba, Arewa Maso Gabas, na cewa Yanbindiga dake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sunyi awon gaba da Mataye biyu da Yara shida na Sarkin Mutum Biyu, dake Karamar Hukumar Gassol, Mai-shari’a Sani Muhammad (Ritaya), a cikin Gidanshi dake Birnin Jaingo. Mai- Martaba Sani Muhammad dai Sarki ne mai daraja ta biyu a Jihar. Rundunar Yansandan Jihar Taraba, a Ranar Juma’ah ta tabbatar da aukuwan mummunan lamarin ga manema labarai a Jalingo a tabakin mai magana…
Cigaba Da KarantawaZan Gina Arewa Da Arzikin Man Da Aka Samu Daga Bauchi – Peter Obi
Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar LP, Mr. Peter Obi, ranar Alhamis, ya tabbatarwa da alummar Jihar Bauchi cewa za ayi amfani da danyen man fetur din aka samu a jihar don ciyar da jihar da kuma yankin Arewa gaba. Ya yi alkawarin ne a yakin neman zaben jam’iyyar da ya gudana a filin wasa na Tafawa Balewa a Bauchi, babban birni Jihar a ranar Alhamis. ”Mun san abin da yake faruwa a Bauchi a halin yanzu. Muna son yin amfani da danyen man da aka hako don cigaban Bauchi,…
Cigaba Da KarantawaKauyawa Sun Fi Kowa Shiga Wahala Kan Sauya Takardun Naira – El-Rufa’i
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya tsawaita wa’adin daina karbar tsoffin takardun kudi cewa lokacin ya yi gajarta da yawa, kuma jama’a na shan wahala sosai. Babban bankin Najeriya dai ya ce za a daina amfani da tsoffin kudade a kasar daga ranar 31 ga watan Janairu lamarin da ya jefa al’umma musamman talakawa a halin wayyo Allah. El-Rufai ya bayyana cewa mutanen karkara da dama wadanda basu da hanyar yin hada-hada kudi sune wadanda wannan hukunci zai fi shafa. Da yake jawabi…
Cigaba Da KarantawaRashin Iya Shugabanci Ne Silar Jefa Najeriya Halin Da Take Ciki – Obasanjo
Tsohon shugaban Æ™asa Olusegun Obasanjo ya ce, babu wani ci gaban da aka samu a jihohin kasar da ke karkashin jagorancin mutane masu rike da matsayin farfesa ko dakta da tsoffin sojoji, har ma da malaman makarantu. Obasanjo ya ce duk da yake an samu wasu jajirtattun shugabannin da ba su da yawa, akasarinsu ba sa iya mulki mai kyau saboda rashin samun mataimaka na gari, abin da ke hana su jagorancin da ake bukata. Tsohon shugaban ya ce, rashin tattaunawa tsakanin shugabannin da masu taimaka musu, kan haifar da…
Cigaba Da KarantawaSauya Takardun Naira: Majalisa Ta Bada Umarnin Kama Gwamnan Babban Banki
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar wakilai ta tarayya ta umurci babban sufetan ‘yan sandan kasar ya kai mata gwamnan babban bankin kasar nan da ranar Talata mai zuwa. Majalisar ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta gayyaci gwamnan babban bankin har sau biyu ba ya zuwa. Wani rahoto na cewa ‘yan majalisar suna so ne su ji daga bakin gwamnan dalilin da ya sa ba za a kara wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun naira ba, wadanda bankin ya ce za su daina…
Cigaba Da Karantawa