2023: Zan Sauya Salon Yaki Da Ta’addanci Idan Na Lashe Zabe – Tinubu

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin sauya salon yakar ‘yan fashin daji da suka addabi mutane idan ya zama shugaban ƙasa a 2023.

An ruwaito cewa tsohon gwamnan na Legas ɗin ya yi wannan furucin ne a wurin taron tattalin arziki da zuba hannun jari karo na Bakwai da ya gudana a garin Kaduna.

Ɗan takarar kujerar shugabancin ƙasa karkashin jam’iyya mai mulki ya kara da cewa yana da tabbacin zai iya jagorantar kasar nan. Haka zalika ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zai magance baki ɗaya matsalolin da suka yi wa ƙasar nan katutu matuƙar suka dangwala masa kuri’u ya zama shugaban ƙasa.

“Idan kuka bar ni a kan dandamalin nan zan ci gaba da kamfe ne, zan roki El-Rufai kar ya bar Najeriya a 2023 domin muna bukatar kwarewarsa a dai-dai wannan lokacin.” “Ina da kwarin guiwar faɗa muku cewa zan iya jagorancin ƙasar nan a 2023 idan kuka goya mun baya. Ina da kwarewar shawo kan baki ɗaya matsalolin nan kuma na dawo da ƙasar nan kan turba mai kyau da ci gaba.”

Labarai Makamanta