Dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga cikin abubuwan da ya shirya wa ‘yan Najeriya idan ya gaji Buhati bayan zaben 2023.
Bola Tinubu yace matukar ‘yan Najeriya suka zabe shi tare da abokin takarar sanata Kashim Shettima, to tabbas goben Najeriya za ta yi kyau ainun, kowa zai yi murna gami da farin ciki.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 28 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa, zai shiga lungu da sakon Najeriya domin tallata hajarsa ga kwadayin darewa kujerar Buhari.
Ya kuma bayyana cewa, yana fatan shi da Shettima su sake sanya fata a zukatan ‘yan Najeriya, tare da yin abubuwan da za su kawo ci gaba ga kasar, da jama’a baki É—aya.
“A shirye muke ni da abokin takara ta domin mu samar da shugabancin da zai habaka kasarmu, ya kuma daukaka martabarta ta hanyan sabon tunani, kirkirar sabbin dabaru da kuma hangen nesa.”
You must log in to post a comment.