2023: Zan Dora Daga Inda Buhari Ya Tsaya – Tinubu

Ɗan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyya mai mulki ta APC Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa zai cigaba da ayyukan Shugaba Buhari idan yayi nasara a shekarar 2023.

Tinubu ya bayyana hakan a jawabin da yayi na fatan alheri ga Buhari a taron bitar ayyukan Ministoci da Sakatarorin din-din-din dake gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ƙara da cewar idan ya ci zabe, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an tarwatsa yan ta’adda a Najeriya da tabbatar da samun tsaro.

Ya yi wa Buhari alkawarin cewa zai karrama dukkan ayyukan da shugaban kasa yayi kuma ba zai watsa masa kasa a ido ba. Ya kara da cewa musamman zai kammala ayyukan gine-gine da gwamnatin Buhari ke yi.

Labarai Makamanta