2023: Zan Bar Najeriya Da Kyau Fiye Da Yadda Na Karɓa A 2015 – Buhari

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa yan Najeriya cewa gwamnatinsa zata miƙa mulkin Najeriya da cigaba fiye da yadda ta ƙarba.

Ya kuma roki mutane su sa Allah a ransu yayin da zasu yi alkalanci kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu zuwa yanzu.

Shugaban ƙasan ya yi wannan jawabin ne yayin ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai domin kaddamar da ayyuka a Kafanchan, Kaduna da Zaria.

Da yake jawabi a fadar mai martaba Sarkin Jema’a, Alhaji Muhammadu Isa II, a Kafanchan, Buhari ya haska maslahar da ya samar wajen karfafa tsarin siyasar ƙasar nan domin rayuwar yan Najeriya ta yi kyau.

Labarai Makamanta