2023: Za Mu Tsayar Da Dan Takarar Da Kowa Zai Yi Na’am Da Shi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana Jam’iyyar APC ta bayyana cewa a lokacin da ya dace, zata fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na 2023 wanda kowa zai amince da shi, abin yarda ga kowane ɗan Najeriya.

Sakataren kwamitin riƙon kwarya na jam’iyya mai mulki, Sanata John Akpanudoehede, shine ya faɗi haka a wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Abuja.

Jawabin ya yi martani ne game da zargin da PDP ta yi cewa shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya na son cigaba da mulki a zagaye na uku.

Sakataren APC ya jaddada cewa jam’iyya ba zata bar wasu ɗai-ɗaikun mutane su dinga juya gwamnatin shugaba Buhari yadda suke so ba, a dai dai lokacin da zaɓen 2023 ke gabatowa, za muyi abin da ya kamata wajen taimakon ƙasa.

A cewar sakataren APC, bayan jam’iyyarsu ta yi gangamin ta na ƙasa zata baiwa jam’iyyar adawa PDP mamaki.

“Bayan babban taron mu na ƙasa, zamu basu mamaki (PDP) idan muka fitar da amintaccen ɗan takarar shugaban ƙasa kuma kowa ya amince da shi, wanda zai ɗaga tutar APC a zaɓen 2023.”

“APC ba ta da kudirin zarcewa zango na uku a kan mulki kamar PDP, abinda muke yi yanzun shine ƙara kafa jam’iyya kuma ba zamu bar wasu ɗai-ɗaikun mutane su dinga juya gwamnatin mu ba.” Bamu da kuduri irin na PDP Sakataren APC ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ba kamar PDP bace domin yanzun PDP tana girban abinda ta shuka a baya ne.

Labarai Makamanta