2023: Za Mu Ƙwace Mulki A Hannun APC – PDP

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta bayyana kwarin gwiwar da take dashi na karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a shekarar 2023.

Sakataren yada labaran PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise akan halin da siyasar Najeriya ke ciki.

Ya ce: “A shiyya daya daga cikin shida, muna da dan takarar mulkin da ke haifar da rashin jituwa wanda tuni kwamitin sulhu karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki yayi sasanci.

“Jam’iyyarmu fata ce ta ‘yan Najeriya kamar yadda muke magana a yau. Ayyukan ta’addanci, tada zaune tsaye, satar mutane sun mamaye al’ummarmu…Hakan ya nuna karara cewa ‘yan Najeriya suna tunanin wanda zai ceci al’ummarmu.

“PDP ta shirya tsaf domin karbar ragamar shugabanci ta hanyar akwatin zabe a 2023.” Ya lura cewa rikicin da ke tsakanin Tsohon Gwamnan Ekiti Ayo Fayose da Gwamnan Oyo Seyi Makinde kwamitin da Saraki ke jagoranta ya warware shi.

Ya ce Saraki ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP na Ogun da na Ekiti kuma ana tattaunawa iri-iri a jam’iyyar. Ya lura cewa karuwar rashin tsaro, ‘yan bindiga da sace dalibai ya nuna akwai bukatar samun sauyi cikin gaggawa.

Labarai Makamanta