2023: ‘Yan Najeriya Ba Su Da Zabin Da Ya Wuce PDP – Atiku

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma ɗan takarar shugaban kasa a ƙarƙashin jam’iyar adawa ta PDP ya ce PDP ce mafita ga Najeriya.

Atiku ya ce PDP ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 16 kafin APC ta amshi mulkin Najeriya a 2015 kuma dukkanin ‘yan Najeriya sun shaida irin alherin da ta shuka wanda har yanzu ana cin gajiyarsa.

Atiku ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Twitter, inda yace, “PDP ce babbar ƙasar jama’ar Najeriya. Duk bangarorin Najeriya suna bukatar jam’iyyar da za ta gyara Najeriya, ba wacce za ta lalata ta ba.

“Jam’iyyar PDP ta tabbatar da za ta gyara Najeriya, sannan ina rokon ‘yan Najeriya da su amince da jam’iyyar don za ta tabbatar da adalci ga kowa.”

Labarai Makamanta