2023: Ya Kamata Buhari Ya Samu Karin Wa’adi Na Uku – Babban Lauya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babban Lauya Robert Clarke (SAN), ya yi kira da a kara wa Shugaba Buhari wa’adin mulki bayan kammala mulkinsa na biyu a 2023.

Babban lauyan, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin ya bayyana cewa watannin da ke gabanin zaben 2023 ba su isa su kawo karshen rashin tsaro ba, balle a iya zabe cikin kwanciyar hankali.

Da yake magana a gidan talabijin na Arise, Clarke ya ƙara da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa shugaban kasa zai iya tsawaita wa’adinsa na tsawon watanni shida, tun da farko, idan yana jin cewa gudanar da zabe zai iya zuwa da tasgaro.

Ya ce ba daidai ba ne a yi
imani cewa Shugaban kasa ba zai iya ci gaba da zama a karagar mulki sama da shekaru takwas na wa’adin mulki biyu ba.

Labarai Makamanta