2023: Tinubu Ya Fi Kowa Cancanta – Yakasai

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Alhaji Tanko Yakasai, wani dattijon kasa daga jihar a ranar Lahadi, 23 ga watan Janairu ya bayyana goyon bayansa ga dan Kudu ya maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshen wa’adinsa a 2023.

An ruwaito cewa, dattijon dan shekaru 96 da haihuwa, ya ce ba zai zama adalci ba a ce yankin Arewa ya ci gaba da yin mulki duk da yunkurin da ‘yan Kudu ke yi na neman kujerar shugabancin kasa.

Dattijon ya ce a tsawon shekarun da ’yan Arewa suka yi mulki a kasar nan ba su tabuka komai ba, illa koma baya da yankin ya faɗa dama ƙasa baki daya.

Ya ci gaba da cewa, a cikin dukkan wadanda suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara daga yankin kudu, jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fi cancanta.

Yakasai ya ce: “Ta yaya za a yi a kullum mu ’yan Arewa ne mu ke mulki? Babu adalci a cikin wannan lamari, mu yi mulki, su (Kudu) su yi mulki shi ne adalci.

“Duk da cewa a tsawon shekarun da ’yan Arewa suka yi mulki ba mu ga komai ba, me za mu ce wa jama’a? Me za mu nuna wa ‘yan Najeriya da suka amfana ko za su amfana domin su ba mu kuri’unsu?.”

Labarai Makamanta