2023: Tinubu Ne Shugaban Kasa – Babban Malamin Addini

Rahotanni daga Ikeja babban birnin Jihar Legas na bayyana cewar Shugaban cocin superintendent of Glorious Vision World Outreach Ministries, Rev (Dr.) David Oyediran, ya yi hasashen cewa babban jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai shugabanci Najeriya a 2023.

A cewar faston, Tinubu na daya daga cikin yan tsirarun mutane da za su iya gyara kasar a matsayin shugaban kasa muddin ya zama shugaban ƙasa a babbar shekarar zaɓe ta 2023.

Fasto Oyediran a jawabinsa mai taken ‘Nufin Allah kan Najeriya’, ya ce Allah ya nuna masa hakan ne bayan yiwa kasar gagarumin addu’a, domin sanin makomar ƙasar a shekarar 2023.

“Allah ya bayyana cewa a cikin yan tsirarun mutanen da za su iya jagoranci da dawo da muradin yan Najeriya shine Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. “Allah ya ce zai jagoranci Najeriya bisa kundin tsarin mulki kuma zai inganta tattalin arzikin kasar. “Allah ya kuma fada mani wasu sakonni na sirri zuwa ya Asiwaju Tinubu wanda za su jagorance shi da taimaka masa wajen cika nauyin da Allah zai daura masa kan Najeriya idan jam’iyyarsa ta zabe shi a matsayin dan takararta.”

Labarai Makamanta