An bayyana cewar Gwamnan Jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal shi ya fi kowane ɗan takarar shugabancin kasa cancanta a babban zabe dake tunkaro mu na shekarar 2023.
Kungiyar Matasa masu rajin samar da kyakkyawan shugabanci a Najeriya ne suka bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da suka kira a Kaduna.
Shugaban Kungiyar Matasan Nasiru Aliyu ya bayyana cewar sai da suka yi karatun ta natsu da tantancewa a tsakanin dukkanin waɗanda suka nuna sha’awa ta fitowa takarar kafin suka fitar da Aminu Tambuwal a matsayin gwarzo.
“Dole a yaba Tambuwal bisa ga kokarin da ya yi na daidaita harkar tsaro a jihar Sokoto, da kuma gudummawar da ya bayar na ciyar da kasa gaba lokacin da yake rike da shugabancin majalisar wakilai, da kasancewar shi amini ga kowa a fadin Najeriya.
Matasan sun kuma bayyana cewar lokaci ya yi da tsofaffi za su kauce su ba matasa dama a bangaren shugabancin kasa, wannan ya sanya suka sake aminta da Aminu Tambuwal kasancewar shi Matashi mai hangen nesa.
You must log in to post a comment.