2023: Tabbas Tinubu Ne Shugaban Kasa – Kingibe

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne shugaban kasar Najeriya na gaba a babban zaben da za a yi na shekarar 2023.

Bola Tinubu dai shine ya yi nasarar lashe tikitin takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC mai mulki a zaben fidda gwaninta da ya gudana a Eagle Square a ranar Laraba, 8 ga watan Yunin shekarar da muke ciki.

Jigon na APC kuma babban jagoran Jam’iyyar ya samu kuri’u 1,271 inda ya kayar da sauran abokan karawarsa su 13 warwas.

A ‘yan kwanaki kafin zaben fidda gwanin na APC, Tinubu ya haddasa cece-kuce lokacin da ya ce shine ya kamata ya zama shugaban kasa na gaba saboda shi ya taimaki shugaban kasa Muhammadu Buhari har ya lashe zaben shugaban kasa na 2015.

Tun bayan da ya lashe tikitin shugaban kasar na APC, tsohon gwamnan na jihar Lagas yana ta ganawa da masu ruwa da tsaki don neman goyon bayansu gabannin babban zaben kasar mai zuwa.

Da yake jawabi a ganawarsa da Tinubu a karshen mako, Kingibe ya ce tsohon gwamnan na jihar Lagas ne zai zama shugaban kasa na gaba saboda sadaukarwarsa.

“Kai ne na gaba. Za ka tashi daga Jagaban Borgu zuwa Jagaban Najeriya; daga Asiwaju na Lagas zuwa Asiwaju na Najeriya. Saboda dukkanin sadaukarwa da ka yi, saboda dukkanin kokarin da ka yi, Allah zai saka maka a wannan lokacin.”

Kingibe dai ya kasance abokin takarar MKO Abiola a zaben shugaban kasa na 1993, amma daga bisani ya yi aiki a karkashin gwamnatin soji na Sani Abacha bayan an soke zaben shugaban kasa na 12 ga watan Yuni.

Labarai Makamanta