2023: Saraki Zai Iya Jagorancin Najeriya – Babangida

Labarin dake shigo mana daga Minna Babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya bayyana goyon bayansa ga tsohon shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki a burinsa na maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Janar Babangida ya yi martani ne kan bukatar da wakilan Abubakar Bukola Saraki da suka samu jagorancin shugaban kungiyar kamfen din sa, Farfesa Hagher Iorwuese da darakta janar, Osaro Onaiwu wadanda suka je har gidan tsohon shugaban da ke Minna domin neman goyon baya.

Babangida wanda ya kasa boye kaunarsa ga Saraki, ya kasa rufe baki don kai tsaye ya ce Saraki tamkar bindigar yaki ce mai harba kanta, a takaice hakan ne kwatancen Saraki, kuma ina da yakinin zai iya jagorancin Najeriya idan ya samu hali.

Kamar yadda yace, ‘yan takara da yawa sun ziyarcesa kuma za su cigaba da zuwa. Amma matashi kamar Saraki wanda ya san kan kasar nan shi ne ya fi dacewa da mulkin kasar nan.

“Na ji dadin samun mutane kamar ku da suka san ma’anar me shugabancin Najeriya ya ke nufi. An rasa wannan ma’anar. Na ji dadi da aka gano wanda zai iya aikin.

Babangida ya jinjinawa kishin kasa na Saraki a matsayinsa na shugaban majalisa na takwas inda yace: “Kokarin Saraki ne ya tseratar da kasar nan har ta tsallake ba ta fada cikin rikici ba. Da ba don shi ba, da Allah kadai ya san abinda zai faru.

Hazakarsa ce ta tseratar da kasar nan, don haka shi ne ya fi dacewa da Najeriya. “Amma kuma akwai jan aiki a gabanmu ta yadda za mu shawo kan ‘yan Najeriya har su yadda da hakan.

Labarai Makamanta